Skip to main content

CAPTIN AHMED MUSA YA AIKEWA ƊAN FIM ƊIN HAUSA BABA KARKUZU TALLAFIN NAIRA 500,000, YA KUMA SA A NEMO KATAFAREN GIDA NA NAIRA MILIYAN 4 ZUWA NAIRA MILIYAN 5 ZAI SAYA MASA

 CAPTIN AHMED MUSA YA AIKEWA ƊAN FIM ƊIN HAUSA BABA KARKUZU TALLAFIN NAIRA 500,000, YA KUMA SA A NEMO KATAFAREN GIDA NA NAIRA MILIYAN 4 ZUWA NAIRA MILIYAN 5 ZAI SAYA MASA.

DAGÀ Shafin Dokin Karfe TV





Shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya, Captin Ahmed Musa MON ya ba da umarnin a Nemo gida wanda kuɗinsa ya kai Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zai sayawa ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu, sannan kuma a yanzu haka ya aike masa da tallafin kuɗi Naira 500,000 domin ya yi cafane duba da halin ƙunci, matsi, gami tsananin rayuwa da ya ke ciki.




Cikin wata tattaunawa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da shi, Captin Ahmed Musa ya bayyana cewa "Na yi magana da Baba Karkuzu ta waya, na kuma tabbatar masa na ba shi tallafin Naira 500,000 ya yi cafane. Bayan haka kuma na shaida masa cewa na ba da umarnin a nemo masa gida na Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zan saya masa daga nan kuma mu ga tayadda zan ƙara taimaka masa". In ji Ahmed Musa.




A ƴan kwanakin nan ne dai aka jiyo tsohon ɗan wasan Hausan, Baba Karkuzu ya na kokawa kan halin ƙunci da ya ke ciki, tayadda har ta kai ya makance ba ya iya gani saboda ƙuncin rayuwa, har ma wasu ke nema masa tallafi a Social Media domin a taimaka masa.




"Sama da shekaru 43 Ina harkar Fim, amma yanzu sai a wayi gari babu abinda za a ci a gidana. Kuma yanzu haka na daina gani, sannan kuma gidan da na ke ciki mai shi ya saka shi a kasuwa", Cewar ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu.




Wannan labarin ya taɓa Captin Ahmed Musa sosai ya yi jimamin halin da Baba Karkuzun ya ke ciki, domin tun ya na yaro a birnin Jos ya ke ganin wasannin Baba Karkuzun a gidan talabijin na NTA. Ganin haka ya sa Captin Ahmed Musa ya nema ya yi magana da shi ta waya ya kuma yi masa wannan albisaahir da wannan tallafi na gida da kuɗi.





Captin Ahmed Musa mutum ne wanda ya yi shuhura wajen taimako da jinƙan al'umma, ko da a baya-bayan nan, ya sayawa wasu matasa mutum 4 manya-manyan gidaje a Kano domin su zauna da iyalansu.

Comments

Popular posts from this blog

YANZU-YANZU: Kutu Ta Baiwa Babban Bankin Nijeriya (CBN) Umarnin Gaggawa Kan Ta Saki Sabbi Da Tsoffin Kudade Domin Al'ummar Nijeriya Su Cigaba Da Amfani Da Su, Inda Tuni Umarnin Kotun Ya Isa Wurin Gwamnan Na CBNAna sa ran daga gobe za a saki kudade domin su soma walwala a hannun al'ummar kasa musamman talakawa da yardar Allah.

Kalli Yadda wani Saurayi Ya Yaudari Budurwa Da Rashin Lafiyarsa Yayi Zina Da Ita Lokacin Da Taje Dubashi

 Tofah Yana Da Kyau lyaye Suna Kula Da Lamarin 'Ya'Yansu A Wannan Zamani, Musamman Yam Matan Yanzu Da Samari Domin Gudu Shiga Tashin Hankalin Rayuwa. Kamar Yadda Muka Samu Wani Bidiyo Daga Shafin Rigar 'Yanchi, Wato Kungiyar Da Take Nemowa Hakkin Duk Mutumin Da Aka Cinyewa Hakkinsa Ko Kuma Aka Zalunta A Jihar Kano, Ta Bayyana Wata Bidiyon Budurwar Data Kawo Karar Saurayinta Bayan Yayi Mata Ciki. Acikin Bayanin Budurwa Ta Bayyana Cewa Saurayinta Ne Yace Mata Bashida Lafiya, Sai Tace Masa Toh Allah Ya Sauka, Sannan Yake Damunta Dacewa Dole Sai Tazo Ta Dubashi Amma Taki Yarda. Sai Daga Karshe Ya Shawo Kanta Tazo Kofar Gidansu Ta Tsaya, Sai Ya Fito Yace Su Shiga Daga Ciki, Anan Ma Bata Yarda Ba Har Dai Ya Samu Tashiga Cikin Gidan Kuma Dakinsa, Yayi Mata Fyade. Bayan Faruwar Wannan Lamari Da Kamar Wata Daya Sai Ta Fara Jin Yanayinta Yana Chanjawa Daga Karshe Aka Gano Cikine Da ita, Aka Bidiye Mahaifan Saurayin Domin Jin Tabakinsu, Har Dai Abun Yakai Ga Ana Zuwa Wajen 'Yan Sa...

Wallahi a wannan yanayin da ake ciki Miliyan 50 tafi min Aljanah Aliyu Naziru

 Wani matashi mai suna Aliyu Naziru ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa "A wannan lokacin da ake ciki yafi son Naira Miliyan 50 a kan Aljanah" Kunji fa ko kuna tare da wannan ra'ayi na Aliyu?