Skip to main content

Innalillahi Ta Kashe Mijin Kawarta Bayan Ya Kama Su Dumu Dumu Suna Madigo A Cikin Gidan Sa

 Ana zargin wata ta kashe mijin kawarta da wuka saboda yake kama su suna aikata mummunan aiki a cikin gidan sa ita da matar shi, wannan abu ya faru ne a wani kauyen jihar anambra. 

Mijin da aka kashe ya kasance yana aiki ne a kwalegin lafiya dake wannan kauye na jihar anambra, sannan an kashe shine bayan ya dawo gida daga aiki lokacin ya tarar da matar da ita kan gado.


Matar shi ta samu damar guduwa bayan da taga mijin na ta ya fadi kasa cikin jini bayan da kawarta ta suka masa wannan wuka. Har yanzu ba’a gano inda take ba amma jami’ai iya kokarinsu.




Mutane sun tabbatar da mijin wanda aka kashe bashi da masaniyar matar shi ta dade tana wannan harka. Yan sanda sun tabbatar da kisan sannan sun kama wacce tayi yanzu haka tana hannun su.





Mijin bai rasu nan take ba sai da aka kai shi asibiti, ya mutu lokacin da likita ke duba shi. Sannan yan sanda sun fara binciken masu aikata irin wannan mummunan laifi.




Sannan nijeriya ta haramta aikata wannan mummunan aiki a kasar.

Comments

Popular posts from this blog

YANZU-YANZU: Kutu Ta Baiwa Babban Bankin Nijeriya (CBN) Umarnin Gaggawa Kan Ta Saki Sabbi Da Tsoffin Kudade Domin Al'ummar Nijeriya Su Cigaba Da Amfani Da Su, Inda Tuni Umarnin Kotun Ya Isa Wurin Gwamnan Na CBNAna sa ran daga gobe za a saki kudade domin su soma walwala a hannun al'ummar kasa musamman talakawa da yardar Allah.