LABARAI DA DUMI-DUMI Aƙalla mutum 2,300 aka tabbatar sun rasu a Reuters Copyright: Reuters Adadin mutanen da suka rasu a Turkiyya ya ƙaru sakamakon girgizar ƙasar da aka yi a yau inda adadin ya kai 1,498, kamaryadda hukumar kare afkuwar bala'i ta ƙasar ta bayyana. Idan aka haɗa jumulla da na girgizar ƙasar da aka yi da asubahi da kuma wadda aka yi da hantsi adadin ya kai 2,300, bayan an sake tabbatar da mutuwar mutum 810 a Syria, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana. Ƙasashe da dama a faɗin duniya dai suna ta jajantawa ƙasashen Turkiyya da Syria tare da yi musu tayin bayar da agaji